quarta-feira, 28 de janeiro de 2015

1 YAH (HAUSA)


Kalman Ya Zama Mutum
1 Tun fil'azal akwai Kalma, Kalman nan kuwa tare da Allah yake, Kalman nan kuwa Allah ne. 2 Shi ne tun fil'azal yake tare da Allah. 3 Dukan abubuwa sun kasance ta gare shi ne, ba kuma abin da ya kasance na abubuwan da suka kasance, sai ta game da shi. 4 Shi ne tushen rai, wannan rai kuwa shi ne hasken mutane. 5 Haske na haskakawa cikin duhu, duhun kuwa bai rinjaye shi ba.
6 Akwai wani mutum da Allah ya aiko, mai suna Yahaya. 7 Shi fa ya zo shaida ne, domin ya shaidi hasken, kowa yă ba da gaskiya ta hanyarsa. 8Ba shi ne hasken ba, ya zo ne domin ya shaidi hasken.
9 Akwai hakikanin haske mai shigowa duniya da yake haskaka kowane mutum. 10 Dā yana duniya, duniyar ta wurinsa ta kasance, duk da haka duniya ba ta san shi ba. 11Ya zo ga abin mulkinsa ne, jama'a tasa kuwa ba ta karɓe shi ba. 12 Amma duk iyakar waɗanda suka karɓe shi, wato, masu gaskatawa da sunansa, ya ba su ikon zama 'ya'yan Allah, 13 wato, waɗanda aka haifa ba daga jini ba, ba daga nufin jiki ko nufin mutum ba, amma daga wurin Allah.
14 Kalman nan kuwa ya zama mutum, ya zauna a cikinmu, yana mai matuƙar alheri da gaskiya. Mun kuma dubi ɗaukakarsa, ɗaukaka ce ta makaɗaicin Ɗa daga wurin Ubansa.
15 Yahaya ya shaida shi, ya ɗaga murya ya ce, “Wannan shi ne wanda na ce, ‘Mai zuwa bayana ya zama shugabana, domin dā ma yana nan tun ba ni.’ ” 16 Dukanmu kuwa daga falala tasa muka samu, alheri kan alheri. 17 Domin Shari'a, ta hannun Musa aka ba da ita, alheri da gaskiya kuwa ta wurin Yesu Almasihu suka kasance. 18 Ba mutumin da ya taɓa ganin Allah daɗai. Makaɗaicin Ɗa, wanda yake yadda Allah yake, wanda kuma yake a wurin Uba, shi ne ya bayyana shi.
Shaidar Yahaya Maibaftisma
(Mat 3.1-12; Mar 1.1-8; Luka 3.1-18)
19 Wannan kuwa ita ce shaidar Yahaya, wato, sa'ad da Yahudawa suka aiki firistoci da Lawiyawa daga Urushalima su tambaye shi, ko shi wane ne. 20 Sai ya faɗi gaskiya, bai yi musu ba, gaskiya ya faɗa ya ce, “Ba ni ne Almasihu ba.” 21 Sai suka tambaye shi, “To, yaya, Iliya ne kai?” Ya ce, “A'a, ba shi ba ne.” Suka ce, “Kai ne annabin nan?” Ya ce, “A'a.” 22Sai suka ce masa, “To, wane ne kai, domin mu sami amsar da za mu mayar wa waɗanda suka aiko mu? Me kake ce da kanka?” 23 Ya ce, “Ni murya ce ta mai kira a jeji, mai cewa, ‘Ku miƙe wa Ubangiji tafarki,’ yadda Annabi Ishaya ya faɗa.”
24Su kuwa, Farisiyawa ne suka aiko su. 25Sai suka tambaye shi suka ce, “To, don me kake yin baftisma in kai ba Almasihu ba ne, ba kuwa Iliya ba, ba kuma annabin nan ba?” 26Sai Yahaya ya amsa musu ya ce, “Ni kam, da ruwa nake baftisma, amma da wani nan tsaye a cikinku wanda ba ku sani ba, 27 shi ne mai zuwa bayana, wanda ko maɓallin takalminsa ma, ban isa in ɓalle ba.” 28 An yi wannan a Betanya ne, a hayin Kogin Urdun, inda Yahaya yake yin baftisma.
“Ga Ɗan Rago na Allah”
29 Kashegari Yahaya ya tsinkayo Yesu na nufo shi, sai ya ce, “Kun ga, ga Ɗan Rago na Allah, wanda zai ɗauke zunubin duniya! 30 Wannan shi ne wanda na ce, ‘Wani yana zuwa bayana, wanda ya zama shugabana, domin dā ma yana nan tun ba ni.’ 31Dā kam, ban san shi ba, sai domin a bayyana shi ga Isra'ila na zo, nake baftisma da ruwa.” 32 Yahaya ya yi shaida ya ce, “Na ga Ruhu na saukowa kamar kurciya daga sama, ya kuma zauna a kansa. 33 Dā kam, ban san shi ba, sai dai wanda ya aiko ni in yi baftisma da ruwa, shi ne ya ce mini, ‘Wanda ka ga Ruhun na sauko masa, yana kuma kasance a kansa, shi ne mai yin baftisma da Ruhu Mai Tsarki.’ 34 Na kuwa gani, na kuma yi shaida, cewa wannan Ɗan Allah ne.”
Almajiran Yesu na Farko
35 Kashegari kuma Yahaya na tsaye da almajiransa biyu. 36 Yana duban Yesu na tafiya, sai ya ce, “Kun ga, ga Ɗan Rago na Allah!” 37Almajiran nan biyu suka ji ya faɗi haka, sai suka bi Yesu. 38 Yesu ya waiwaya ya ga suna biye da shi, sai ya ce musu, “Me kuke nema?” Suka ce masa, “Ya Rabbi, wato Malam ke nan, ina kake da zama?” 39Sai ya ce musu, “Ku zo ku gani.” Sai suka je suka ga inda yake da zama, suka kuwa yini tare da shi. Wajen ƙarfe huɗu na yamma ne kuwa. 40Ɗaya daga cikin biyun nan da suka ji maganar Yahaya suka kuma bi Yesu, Andarawas ne, ɗan'uwan Bitrus. 41 Sai ya fara samo ɗan'uwansa Bitrus, ya ce masa, “Mun sami Almasihu,” wato shafaffe. 42 Sai ya kai shi wurin Yesu. Yesu ya dube shi, ya ce, “Wato kai ne Saminu ɗan Yahaya? Za a kira ka Kefas,” wato Bitrus.
Yesu Ya Kira Filibus da Nata'ala
43 Kashegari Yesu ya yi niyyar zuwa ƙasar Galili. Sai ya sami Filibus, ya ce masa, “Bi ni.” 44 Filibus kuwa mutumin Betsaida ne, garin su Andarawas da Bitrus. 45 Filibus ya sami Nata'ala, ya ce masa, “Mun sami wanda Musa ya rubuta labarinsa a Attaura, annabawa kuma suka rubuta labarinsa, wato Yesu Banazare, ɗan Yusufu.” 46 Nata'ala ya ce masa, “A iya samun wani abin kirki a Nazarat kuwa?” Sai Filibus ya ce masa, “Taho dai, ka gani.” 47 Yesu ya ga Nata'ala na nufo shi, sai ya yi zancensa ya ce, “Kun ga, ga Ba'isra'ile na gaske wanda ba shi da ha'inci!” 48Nata'ala ya ce masa, “A ina ka san ni?” Yesu ya amsa masa ya ce, “Tun kafin Filibus ya kira ka, sa'ad da kake gindin ɓaure, na gan ka.” 49 Sai Nata'ala ya amsa masa ya ce, “Ya Shugaba, kai Ɗan Allah ne! Kai Sarkin Isra'ila ne!” 50Yesu ya amsa ya ce, “Wato, domin na ce maka na gan ka a gindin ɓaure ne kake ba da gaskiya? Ai, za ka ga al'amuran da suka fi haka ma.” 51 Yesu kuma ya ce masa, “Lalle hakika, ina gaya muku, za ku ga sama ta dāre, mala'ikun Allah suna hawa da sauka ga Ɗan Mutum.”
 
 
Biki a Kana ta Galili
1 A rana ta uku sai aka yi bikin aure a Kana ta ƙasar Galili. Uwar Yesu kuwa tana nan, 2aka kuma gayyaci Yesu da almajiransa. 3Da ruwan inabi ya gaza, uwar Yesu ta ce masa, “Ba su da sauran ruwan inabi.” 4 Yesu ya ce mata, “Iya, ai, wannan magana ba taki ba ce. Lokacina bai yi ba tukuna.” 5 Sai uwa tasa ta ce wa barorin, “Duk abin da ya ce ku yi, sai ku yi.” 6 A wurin kuwa akwai randuna shida na dutse a ajijjiye, bisa ga al'adar Yahudawa ta tsarkakewa, kowacce na cin wajen tulu shida shida. 7Sai Yesu ya ce musu, “Ku cika randunan nan da ruwa.” Suka ciccika su fal. 8Sa'an nan ya ce musu, “To, yanzu ku ɗiba, ku kai wa uban bikin.” Sai suka kai. 9 Da uban bikin ya kurɓi ruwan da yanzu aka mayar ruwan inabi, bai kuwa san inda aka samo shi ba (amma barorin da suka ɗebo ruwan sun sani), ya yi magana da ango, 10ya ce, “Kowa, ai, kyakkyawan ruwan inabi yakan fara bayarwa, bayan mutane sun shassha, sa'an nan kuma ya kawo wanda ya gaza na farin kyau. Amma kai ka ɓoye kyakkyawan ruwan inabin sai yanzu!”
11 Wannan ce mu'ujizar farko da Yesu ya yi, ya kuwa yi ta ne a Kana ta ƙasar Galili, ya bayyana ɗaukakarsa. Almajiransa kuma suka gaskata da shi.
12 Bayan haka sai ya tafi Kafarnahum, da shi da uwa tasa, da 'yan'uwansa, da kuma almajiransa, suka zauna a can 'yan kwanaki.
Yesu Ya Tsabtace Haikali
(Mat 21.12-13; Mar 11.15-17; Luka 19.45-46)
13 Idin Ƙetarewa na Yahudawa ya matso, sai Yesu ya tafi Urushalima. 14A cikin Haikali ya sami waɗansu dillalan shanu, da na tumaki, da na tattabarai, da kuma 'yan canjin kuɗi zaune wurin aikinsu. 15Sai ya tuka bulala mai harsuna ta igiya, ya kore su duka daga Haikalin, har da tumakin da shanun, ya kuma watsar da kuɗin 'yan canjin, ya birkice teburorinsu. 16 Ya ce da dillalan tattabarai, “Ku kwashe waɗannan daga nan, kada ku mai da Haikalin Ubana kasuwa.” 17 Sai almajiransa suka tuna a rubuce yake cewa, “Kishin Haikalinka ya ci raina matuƙa.” 18 Sai Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Wace mu'ujiza za ka nuna mana da kake haka?” 19 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku rushe Haikalin nan, ni kuwa in ta da shi a cikin kwana uku.” 20Yahudawa suka ce, “Sai fa da aka shekara arba'in da shida ana ginin Haikalin nan, kai kuwa a cikin kwana uku za ka ta da shi?” 21 Amma haikalin da Yesu ya ambata jikinsa ne. 22 Saboda haka bayan an tashe shi daga matattu, almajiransa suka tuna ya faɗi haka, suka kuma gaskata Nassi da maganar da Yesu ya faɗa.
Yesu Ya San Zuciyar Kowa
23 To, sa'ad da yake Urushalima lokacin Idin Ƙetarewa, mutane da yawa suka gaskata da sunansa, saboda ganin mu'ujizan da ya yi. 24Amma Yesu bai amince da su ba, 25 domin ya san zuciyar kowa, ba kuma sai wani ya shaidi mutum a wurinsa ba, domin shi kansa ya san abin da yake zuciyar ɗan adam.
 
 
Yesu da Nikodimu
1 To, akwai wani Bafarisiye, sunansa Nikodimu, wani shugaban Yahudawa. 2 Wannan mutum ya zo wurin Yesu da dad dare, ya ce masa, “Ya Shugaba, mun sani kai malami ne da ka zo daga wurin Allah, domin ba mai iya yin waɗannan mu'ujizan da kake yi, sai ko Allah yana tare da shi.” 3 Yesu ya amsa masa ya ce, “Lalle hakika, ina gaya maka, in ba a sāke haifar mutum ba, ba zai iya ganin Mulkin Allah ba.” 4Nikodimu ya ce masa, “Ƙaƙa za a haifi mutum bayan ya tsufa? Wato, ya iya komawa a cikin uwa tasa ta sāke haifo shi?” 5 Yesu ya amsa masa ya ce, “Lalle hakika, ina gaya maka, in ba an haifi mutum ta ruwa da kuma Ruhu ba, ba zai iya shiga Mulkin Allah ba. 6 Abin da mutum ya haifa mutum ne, abin kuma da Ruhu ya haifa ruhu ne. 7Kada ka yi mamaki domin na ce maka, ‘Dole a sāke haifarku.’ 8Iska tana busawa inda ta ga dama. Kakan ji motsinta, amma ba ka san inda ta fito da inda za ta. Haka fa yake ga duk wanda Ruhu ya haifa.” 9 Sai Nikodimu ya amsa masa ya ce, “Ƙaƙa wannan zai yiwu?” 10 Yesu ya amsa masa ya ce, “Ashe, kai ma da kake malamin Isra'ila, ba ka fahimci waɗannan al'amura ba? 11 Lalle hakika, ina gaya maka, abin da muka sani shi muke faɗa, muna kuma shaidar da abin da muka gani, amma kun ƙi yarda da shaidarmu. 12In na yi muku zancen al'amuran duniya ba ku gaskata ba, yaya za ku gaskata in na yi muku zancen al'amuran sama? 13 Ba wanda ya taɓa hawa cikin Sama sai shi wanda ya sauko daga Sama, wato, Ɗan Mutum da yake Sama. 14 Kamar yadda Musa ya ɗaga macijin nan a jeji, haka kuma dole ne a ɗaga Ɗan Mutum, 15 domin duk wanda ya gaskata da shi, ya sami rai madawwami.
16 “Saboda ƙaunar da Allah ya yi wa duniya har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya hallaka, sai dai ya sami rai madawwami. 17 Gama Allah bai aiko Ɗansa duniya domin yă yanke mata hukunci ba, sai dai domin duniya ta sami ceto ta wurinsa. 18 Duk wanda ya gaskata da shi, ba za a yi masa hukunci ba. Wanda kuwa bai ba da gaskiya ba, an riga an yi masa hukunci, domin bai gaskata da sunan makaɗaicin Ɗan Allah ba. 19 Hukuncin kuwa shi ne, haske ya shigo duniya, amma mutane suka fi ƙaunar duhu da hasken, don ayyukansu mugaye ne. 20 Duk mai yin rashin gaskiya yakan ƙi hasken, ba ya kuma zuwa wajen hasken, don kada ayyukansa su tonu. 21Mai aikata gaskiya kuwa yakan zo wajen hasken, domin a bayyana ayyukansa, cewa, da taimakon Allah ne aka yi su.”
Shi Lalle Ya Riƙa Ƙaruwa, Ni kuwa Raguwa
22 Bayan haka, Yesu da almajiransa suka tafi ƙasar Yahudiya. A nan ya jima da su, yana yin baftisma. 23Yahaya kuma yana yin baftisma a Ainon kusa da Salima, domin da ruwa da yawa a can. Mutane kuwa suka yi ta zuwa ana yi musu baftisma. 24 Domin a sa'an nan ba a sa Yahaya a kurkuku ba tukuna.
25 Sai fa almajiran Yahaya suka tasar wa wani Bayahude da muhawara a kan maganar tsarkakewa. 26 Suka kuma zo wurin Yahaya, suka ce masa, “Ya shugaba, wanda dā kuke tare a hayin Kogin Urdun, wanda kai kanka ma ka shaida shi, to, ga shi, yana yin baftisma, har kowa da kowa yana zuwa wurinsa.” 27Sai Yahaya ya amsa ya ce, “Ba mai iya samun kome sai ko an ba shi daga Sama. 28 Ku kanku ma shaiduna ne a kan na ce ba ni ne Almasihu ba, amma an aiko ni ne ni riga shi gaba. 29 Mai amarya shi ne ango. Abokin ango kuwa da yake tsaye, yake kuma sauraron magana tasa, yakan yi farin ciki ƙwarai da jin muryar angon. Saboda haka farin cikin nan nawa ya cika. 30Shi kam, lalle ne ya riƙa ƙaruwa, ni kuwa in riƙa raguwa.
Wanda Ya Zo daga Sama
31 “Mai zuwa daga Sama yana Sama da kowa. Wanda yake na ƙasa asalinsa kuwa na ƙasa ne, maganar ƙasa kuma yake yi. Mai zuwan nan daga Sama yana Sama da kowa. 32 Abin da ya ji, ya kuma gani, shi yake shaidarwa, duk da haka ba wanda yake yarda da shaidarsa. 33Duk wanda ya yarda da shaidarsa, ya haƙƙaƙe, cewa, Allah mai gaskiya ne. 34 Domin wanda Allah ya aiko, zantuttukan Allah yake faɗa, gama Allah yana ba da Ruhu ba da iyakancewa ba. 35 Uban yana ƙaunar Ɗan, ya kuma sa kome a hannunsa. 36 Wanda ya gaskata da Ɗan, yana da rai madawwami. Wanda ya ƙi bin Ɗan kuwa, ba zai sami rai ba, sai dai fushin Allah ya tabbata a gare shi.”
 
 
Yesu da Wata Basamariya
1 To, da Ubangiji Yesu ya sani dai Farisiyawa sun ji labari yana samun almajirai, yana kuma yi musu baftisma fiye da Yahaya 2(ko da yake dai ba Yesu kansa yake yin baftisma ba, almajiransa ne), 3 sai ya bar ƙasar Yahudiya, ya koma ƙasar Galili. 4Lalle ne kuwa yă ratsa ƙasar Samariya. 5 Sai ya zo wani gari na ƙasar Samariya, wanda ake kira Saikar, kusa da yankin ƙasar da Yakubu ya ba ɗansa Yusufu. 6Rijiyar Yakubu kuwa a nan take. Saboda gajiyar tafiya fa, sai Yesu ya zauna haka nan a bakin rijiyar. Wajen tsakar rana ce kuwa.
7Sai ga wata Basamariya ta zo ɗiban ruwa. Yesu ya ce mata, “Sa mini ruwa in sha.” 8 Almajiransa kuwa sun shiga gari sayen abinci. 9 Sai Basamariyar ta ce masa, “Ƙaƙa kai Bayahude za ka roƙe ni ruwan sha, ni da nake Basamariya?” (Don Yahudawa ba sa cuɗanya da Samariyawa). 10 Yesu ya amsa mata ya ce, “Da kin san kyautar Allah, da kuma wanda ya ce miki, ‘Sa mini ruwa in sha,’ ai, da kin roƙe shi, shi kuwa zai ba ki ruwan rai.” 11Sai matar ta ce masa, “Ya Shugaba, ai, ba ka da guga, rijiyar kuwa da zurfi. To, ina ka sami ruwan nan na rai? 12 Ashe, ka fi ubanmu Yakubu ne, wanda ya bar mana rijiyar, har shi da kansa, da 'yayansa, da dabbobinsa, suka sha ruwanta?” 13Yesu ya amsa mata ya ce, “Duk mai shan ruwan nan zai sāke jin ƙishirwa. 14 Amma duk wanda ya sha ruwan da zan ba shi, ba zai ƙara jin ƙishirwa ba har abada. Ruwan da zan ba shi kuwa zai zama maɓuɓɓuga a gare shi, yana ɓuɓɓugowa har ya zuwa rai madawwami.” 15 Matar ta ce masa, “Ya Shugaba, ka ba ni ruwan nan, don kada in ƙara jin ƙishirwa, kada kuma in riƙa zuwa har nan in ɗiba.”
16Sai Yesu ya ce mata, “Je ki, ku zo da mijinki.” 17Sai matar ta amsa ta ce, “Ai, ba ni da miji.” Yesu ya ce mata, “Gaskiyarki da kika ce ba ki da miji, 18don kin auri maza biyar, wanda kuke tare yanzu kuwa ba mijinki ba ne. A nan kam kin yi gaskiya.” 19 Matar ta ce masa, “Ya Shugaba, na dai gane kai annabi ne. 20 Kakanninmu sun yi sujada a dutsen nan. Ku kuwa kun ce a Urushalima ne wurin da ya wajaba a yi sujada yake.” 21 Sai Yesu ya ce mata, “Uwargida, ki gaskata ni, lokaci na zuwa da ba za ku yi wa Uba sujada ba, ko a kan dutsen nan, ko a Urushalima, 22 Ku kuna yi wa abin da ba ku sani ba sujada, mu kuwa muna yi wa abin da muka sani sujada, domin ceto ta hanyar Yahudawa yake. 23 Amma lokaci na zuwa, har ma ya yi, da masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada a ruhu, da gaskiya kuma. Lalle kuwa irin waɗannan masu sujada ne Uba yake nema. 24 Allah Ruhu ne, masu yi masa sujada kuwa lalle su yi masa sujada a ruhu, da gaskiya kuma.” 25 Sai matar ta ce masa, “Na san Masihi yana zuwa, wanda ake kira Almasihu. Sa'ad da ya zo kuwa, zai sanar da mu kome.” 26 Yesu ya ce mata, “Ni ne, ni mai maganan nan da yake.”
27 Nan take almajiransa suka dawo. Suka yi mamakin ganin yana magana da mace. Amma kuwa ba wanda ya ce, “Me kike bukata?” ko, “Don me kake magana da ita?” 28Sai matar ta bar tulunta, ta koma gari, ta ce wa mutane, 29 “Ku zo, ku ga mutumin da ya gaya mini duk abin da na taɓa yi! Shin, ko wannan shi ne Almasihu?” 30Sai suka fito daga garin suka nufo shi.
31 Ana cikin haka sai almajiran suka roƙe shi suka ce, “Ya shugaba, ci abinci.” 32Amma ya ce musu, “Ina da abincin da ba ku sani ba.” 33Almajiran suka ce wa juna, “Shin, wani ya kawo masa abinci ne?” 34 Sai Yesu ya ce musu, “Abincina shi ne in aikata nufin wanda ya aiko ni, in kuma cika aikinsa. 35 Ba kuna cewa, kaka saura wata huɗu ba? Ina gaya muku fa, ku duba gonaki, ku gani, sun nuna sun isa girbi. 36 Mai girbi na samun lada, yana kuma tara amfani zuwa rai madawwami, domin mai shuka da mai girbi su yi farin ciki tare. 37 A nan kam, wannan karin maganar gaskiya ne cewa, ‘Wani da shuka, wani da girbi.’ 38Na aike ku girbin abin da ba ku yi wahalarsa ba. Waɗansu sun yi wahala, ku kuwa kun mori wahalarsu.”
39 Samariyawa da yawa na wannan gari suka gaskata da shi saboda maganar matan nan da ta ce, “Ya gaya mini duk abin da na taɓa yi.” 40Da Samariyawa suka iso wurinsa, suka roƙe shi ya sauka a wurinsu. Ya kuwa kwana biyu a nan. 41Waɗansu kumma da yawa fiye da na dā suka ba da gaskiya saboda magana tasa. 42 Sa'an nan suka ce wa macen, “Yanzu kam, mun ba da gaskiya, ba don abin da kika faɗa kawai ba, domin mu ma mun ji da kanmu, mun kuma tabbata lalle wannan shi ne Mai Ceton duniya.”
Yesu Ya Warkar da Ɗan Bafada
43 Bayan kwana biyun nan sai ya tashi daga nan ya tafi ƙasar Galili. 44 Domin Yesu kansa ya yi shaida cewa annabi ba shi da girma a ƙasarsu. 45 Da ya isa ƙasar Galili, sai Galilawa suka yi na'am da shi, domin sun ga duk abin da ya yi a Urushalima a lokacin idi, domin su ma sun je idin.
46 Sai ya sāke zuwa Kana ta ƙasar Galili, inda ya mai da ruwa ruwan inabi. A Kafarnahum kuwa akwai wani bafada wanda ɗansa ba shi da lafiya. 47 Da jin cewa Yesu ya fito ƙasar Yahudiya ya komo ƙasar Galili, sai ya tafi wurinsa, ya roƙe shi ya je ya warkar da ɗansa, don yana bakin mutuwa. 48 Yesu ya ce masa, “In ba mu'ujizai da abubuwan al'ajabi kuka gani ba, ba yadda za a yi ku ba da gaskiya.” 49Sai bafadan nan ya ce masa, “Ya Shugaba, ka zo tun ƙaramin ɗana bai mutu ba.” 50Yesu ya ce masa, “Yi tafiyarka, ɗanka a raye yake.” Mutumin kuwa ya gaskata maganar da Yesu ya faɗa masa, ya yi tafiyarsa. 51Yana cikin tafiya sai ga barorinsa sun taryo shi, suka ce masa, “Ɗanka a raya yake.” 52Sai ya tambaye su ainihin lokacin da ya fara samun sauƙi. Suka ce masa, “Jiya da ƙarfe ɗaya na rana zazzaɓin ya sake shi.” 53 Sai uban ya gane, daidai lokacin nan ne, Yesu ya ce masa, “Ɗanka a raye yake.” Shi da kansa kuwa ya ba da gaskiya, da jama'ar gidansa duka. 54 Wannan kuwa ita ce mu'ujiza ta biyu da Yesu ya yi, bayan Komowarsa ƙasar Galili daga ƙasar Yahudiya.
 
 
Warkarwa a Tafkin Betasda
1Bayan haka aka yi wani idi na Yahudawa, Yesu kuwa ya tafi Urushalima.
2 A Urushalima, kusa da Ƙofar Tumaki, akwai wani ruwa da ake ce da shi Betasda da Yahudanci, an kuwa kewaye shi da shirayi biyar. 3A shirayin nan kuwa marasa lafiya da yawa sun saba kwanciya, makafi, da guragu, da shanyayyu. [Suna jira a motsa ruwan. 4Don lokaci lokaci wani mala'ika yakan sauko cikin ruwan ya motsa shi. Duk kuwa wanda ya fara shiga bayan an motsa ruwan, sai ya warke daga duk irin cutar da yake da ita.] 5A nan kuwa akwai wani mutum da ya shekara talatin da takwas da rashin lafiya. 6Da Yesu ya gan shi kwance, ya kuma sani ya daɗe da wannan hali, sai ya ce masa, “Kana so a warkar da kai?” 7Marar lafiyar ya amsa masa ya ce, “Ya Shugaba, ai, ba ni da wanda zai angaza ni cikin ruwan lokacin da aka motsa shi. Lokacin da na doshi ruwan kuma sai wani ya riga ni shiga.” 8 Sai Yesu ya ce masa, “Tashi, ka ɗauki shimfiɗarka, ka yi tafiya!” 9 Nan take mutumin ya warke, ya ɗauki shimfiɗarsa ya yi tafiya tasa.
Ran nan kuwa Asabar ce. 10 Saboda haka Yahudawa suka ce da wanda aka warkar ɗin, “Ai, Asabar ce, bai kuwa halatta ka ɗauki shimfiɗarka ba.” 11Sai ya amsa musu ya ce, “Ai, wanda ya warkar da ni, shi ne ya ce in ɗauki shimfiɗata, in tafi.” 12Suka tambaye shi, “Wane mutum ne ya ce maka ka ɗauki shimfiɗarka ka tafi?” 13Wanda aka warkar ɗin kuwa bai san ko wane ne ba, domin Yesu ya riga ya tashi saboda taron da yake wurin. 14 Bayan haka Yesu ya same shi a Haikali, ya ce masa, “Ka ga fa, ka warke! To, ka daina yin zunubi, don kada wani abu da ya fi wannan muni ya same ka.” 15 Sai mutumin ya tafi ya gaya wa Yahudawa, Yesu ne ya warkar da shi. 16Saboda haka, Yahudawa suka fara tsananta wa Yesu, don yana yin irin waɗannan abubuwa ran Asabar. 17 Yesu kuwa ya amsa musu ya ce, “Ubana yana aiki har yanzu, ni ma ina yi.” 18 Don haka, Yahudawa suka ƙara nema su kashe shi, ba don ya keta Asabar kaɗai ba, har ma domin ya ce Allah Ubansa ne, wato, yana daidaita kansa da Allah.
Ikon Ɗan
19 Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, Ɗan ba ya yin kome shi kaɗai, sai abin da ya ga Uba yana yi. Domin duk abin da Uban yake yi, haka shi Ɗan ma yake yi. 20 Domin Uban na ƙaunar Ɗan, yana kuma nuna masa duk abin da shi kansa yake yi, har ma zai nuna masa ayyukan da suka fi waɗannan, domin ku yi al'ajabi. 21 Yadda Uba yake ta da matattu ya kuma raya su, haka Ɗan ma yake rayar da wanda ya nufa. 22 Uba ba ya hukunta kowa, sai dai yā danƙa dukkan hukunci ga Ɗan, 23 domin kowa yă girmama Ɗan, kamar yadda ake girmama Uban. Wanda ba ya girmama Ɗan, ba ya girmama Uban da ya aiko shi ke nan. 24 Lalle hakika, ina gaya muku, duk mai jin maganata, yake kuma gaskata wanda ya aiko ni, yana da rai madawwami. Ba za a yi masa hukunci ba, domin ya riga ya tsere wa mutuwa, ya kai ga rai.
25 “Lalle hakika, ina gaya muku, lokaci na zuwa, har ma ya yi, da matattu za su ji muryar Ɗan Allah, masu ji kuwa su rayu. 26Yadda Uba kansa yake tushen rai, haka ya sa Ɗan ya zama tushen rai. 27 Ya kuma ba shi ikon zartar da hukunci, saboda shi Ɗan Mutum ne. 28 Kada ku yi mamakin wannan, domin lokaci na zuwa da duk waɗanda suke kaburbura za su ji murya tasa, 29 su kuma fito, waɗanda suka aikata nagarta su tashi, tashin rai, waɗanda suka yi rashin gaskiya kuwa su tashi, tashin hukunci.
Shaidun Yesu
30 “Ba na iya yin kome ni kaɗai. Yadda nake ji, haka nake yin hukunci. Hukuncina kuwa na adalci ne, domin ba nufin kaina nake bi ba, sai dai nufin wanda ya aiko ni. 31 In na shaida kaina, shaidata ba tabbatacciya ba ce. 32 Akwai wani mashaidina dabam, na kuwa san shaidar da yake yi mini tabbatacciya ce. 33 Kun aika wajen Yahaya, shi kuma ya shaidi gaskiya. 34 Duk da haka shaidar da na dogara da ita ba ta mutum ba ce. Na dai faɗi haka ne domin ku sami ceto. 35 Yahaya fitila ne mai ci, mai haske kuma, kun kuwa yarda ku yi farin ciki matuƙa da haskensa ɗan lokaci kaɗan. 36 Amma shaidar da ni nake da ita ta fi ta Yahaya ƙarfi. Domin ayyukan da Uba ya ba ni in gama, su ainihin ayyukan nan da nake yi, ai, su ne shaidata a kan cewa, Uba ne ya aiko ni. 37 Uban kuma da ya aiko ni, shi kansa ya shaide ni. Ba ku taɓa jin muryarsa ba, ko ganin kama tasa. 38 Maganarsa kuwa ba ta zauna a zuciyarku ba, domin ba ku gaskata wanda ya aiko ni ba. 39 Kuna ta nazarin Littattafai, don a tsammaninku a cikinsu za ku sami rai madawwami, alhali kuwa su ne suke shaidata. 40Duk da haka, kun ƙi zuwa wurina ku sami rai. 41 Ba na karɓar girma wurin mutane. 42Amma fa na san ku, ba ku da ƙaunar Allah a zuci. 43Ni na zo ne da sunan Ubana, ga shi, ba ku karɓe ni ba. In da wani zai zo da sunan kansa, shi za ku karɓa. 44 Ta yaya za ku ba da gaskiya, ku da kuke karɓar girma a junanku, girman da yake daga Allah Makaɗaici kuwa, ba kwa nemansa? 45 Kada ku zaci zan yi ƙararku wurin Uba. Akwai mai yin ƙararku, shi ne Musa, wanda kuke dogara da shi. 46 Da dai kun gaskata Musa, da kun gaskata ni, domin labarina ya rubuta. 47 In kuwa ba ku gaskata abin da ya rubuta ba, ta yaya za ku gaskata maganata?”
 
 https://www.bible.com/pt/bible/71/jhn.1

Nenhum comentário:

Postar um comentário